Babu kokwanto cewa duk wanda Allah ya daukaka a addini ko a duniya to da akwai sa hannunmu mu mata, ko ta hanyar tarbiya a matsayin uwaye, ko kuma karfafa guiwa da taimako a matsayin mai daki. Ga wasu ‘yan shawarwari domin karfafa guiwar mai gidanki har hakansa ya cimma ruwa ya sami yardar Allah a gidan aljanna.
1- Ki san bangaren da mai gidanki yake da wata baiwa, kwarewa … domin ki karfafe shi, ki ba shi shawarwari, ki yabe shi, tare da yi masa addu’ar dorewa da kariya.
2- Ki san bangarorin da yake da rauni a cikinsu domin ki taya shi magance su. Kar ki ingiza mai kantu cikin ruwan mutuwar jiki da kasala da cutar son duniya.
3- Daga himmar mai gidanki sama, ki taimaka masa ya shiga cikin – ko ma gaba-gaban – masu rige-rige cikin ayyukan alheri, ya zama mai amfanarwa ne ga al’ummar Annabi (s.a.w).
A karshe, kar ki manta cewa: Allah ba ya tozarta duk wani kokarin mai kokari ko mai kankantarsa. Allah ya ce: Tashi in taimake ka! Saboda haka kada ki rena duk wata dama da kika samu cikin alheri. Ko ya motsi yake ya fi labewa.
Nafisatu Abubakar (Umm Abdallah)