Habaka son Allah da manzonsa a zukatan yara ba karamin mahimmanci ne da shi ba, don wannan zai sa su rika bin Allah da manzonsa sau-da-kafa, a komai wanda wannan ya hada da biyayya ga iyayensu. Wasu daga cikin hanyoyin dasa wa yara ko habaka kaunar Allah a zukatansu su ne:
1. Iyaye su rika nuna son Allah a mu’amalarsu
2. A rika yi wa yaro bayanin waye
3. Gaya wa yaro ni’imomin da Allah ya yi masa
4. Gayawa yaro cewa komai Allah ne yake bayarwa
5. Gaya yaro kyautar da Allah ya shirya wa mai yi masa biyayya
Zainab Ibrahim