‘Yar uwa! Kada ki manta da cewa duk mai rai fa zai mutu, kuma kowa zai shiga kabari, kabari kuwa dayan biyu ne, ko dai ya zama gidan ni’ima, gidan dadi da yalwa, kuma a fadadawa dan aljanna kabarinsa gwargwadon zira’i saba’in zai kasance cikin ni’ima har zuwa tashin alkiyama. Ko kuma ya kasance gidan azaba da kunci da wahala, za’a rika yi masa azaba tun daga kabarin ana kuma dukansa da guduma ta wuta. Kuma za’a kuntata masa kabarin a matse shi har kasusuwansa su rika kara, wanda da mutanen duniya za su ji da sun narke saboda tsananin firgita.Bayan kwanciyar kabari na iya shekarun da Allah ya kaddara, za’a tayar da mutane su tashi a firgice cikin dimuwa, kowa yana gudu ba tare da ya san inda ya nufa ba. Sannan a gurfanar da mutane a gaban Allah (SWT) wanda babu wani sarki a wannan ranar sai shi.Laa ilaha illallah! Hakika wannan rana ce ta tonon asiri, ranar tonon silili, ranar da babu abin da zai boyu sai an bayyana shi. Allah muna rokon ka ka kiyaye mu ka fitar da mu daga azaba, da tsoro da firgita na wannan rana, amin.‘Yar uwa bayan wannan hisabi, kowa za’a ba shi masaukinsa da ya dace da ayyukansa a mazauni na dauwama guda biyu; ko dai aljanna wadda fadinta ya kai nisan dake tsakanin sama da kasa. Ko kuma wuta mai tsananin zafi wadda har sashenta yana cinye sashe. Allah ka nisanta mu daga wuta, ka tserar da mu amin. Mai rabo shi zai shiga aljanna, Allah ka sa muna da rabo a cikinta da iyayenmu, da mazajenmu da ‘ya’ya da duk zuriyarmu, da duk musulmi baki daya. Marar rabo kuma wanda ya butulce wa ubangijinsa, ya bi son zuciyarsa, wannan wuta ce makomarsa. Allah (SWT) yana cewa:“Duk wanda ya kubuta daga wuta kuma aka shigar da shi aljanna hakika ya rabauta” (Ali Imran 85).Ya ke ‘yar uwa! Hakika bana shakkar cewa kina kaunar samun wannan babban rabo; don haka kada ki kuskura ki yaudari kanki, ko a yaudare ki, aljanna ta wadanda suka yi aikin kwarai ce, yin imani da ayyuka na kwarai su suke isar da mutum kofofin aljanna, kuma karantar Alkur’ani shi ne tsanin da ake hawa benayen aljanna.Saboda haka ‘yar uwa, ki nisanci duk wasu shaidanu da na ambata miki ire iren su a baya wadanda a ko yaushe suke son su ga kin yi wa Allah tawaye ki bata, kuma ki halaka. Ki toshe kunnuwanki daga duk wani kiran ‘yanci ko hudubar shaidan da za su rada miki, ki ce musu Ahir dinku.Ki zama baiwar Allah ta gari, mai tarbiyyantar da ‘ya’ya na gari wadanda za su zama manyan gobe. Ki zama babban jigo na gina wannan al’umma, kada ki zama hanyar ruguza ta.A karshe nake kara jaddada mana cewa yin riko da Alkur’ani da sunna shi ne zai kai mu ga gaci muddin mun rike su ba za mu bata ba, ba kuma za mu tozarta ba, a nan duniya, kuma a lahira mu samu sakamako mai girma. Allah ya sa mu dace Amin.Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka bamu ikon bin ta, muyi aiki da ita, Ka nuna mana karya Ka ba mu ikon guje mata. Allah Ka ba mu aljanna don rahamarKa, Ka nisantar da mu daga wuta. Allah Ka jikan iyayenmu da kakanninmu da ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu, da duk musulmi baki daya. Allah Ka yafe mana kura-kuran mu Amin.
Safiyyah Hussain Falaki