“Me ya hada ni da Matar wani!”

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude ya saki matarsa, kafin ta gama idda sai wasu suka zo takanas suka tambaye shi Me ya hada ku da wance ne har ka sake ta?

Sai ya ce: “

Mai hankali ba ya tona asirin matarsa”

Bayan ta gama iddar-ke nan ta fita daga hannunsa- sai suka kuma yi masa waccan tambayar dai, sai ya ce:

“Me ya hada ni da matar wani!”

Me ake koya a wannan kissa?

Published in: on February 9, 2008 at 12:46 pm Leave a Comment

MATA IYAYEN GIJI!

Babu kokwanto cewa duk wanda Allah ya daukaka a addini ko a duniya to da akwai sa hannunmu mu mata, ko ta hanyar tarbiya a matsayin uwaye, ko kuma karfafa guiwa da taimako a matsayin mai daki. Ga wasu ‘yan shawarwari domin karfafa guiwar mai gidanki har hakansa ya cimma ruwa ya sami yardar Allah a gidan aljanna.

1-  Ki san bangaren da mai gidanki yake da wata baiwa, kwarewa … domin ki  karfafe shi, ki ba shi shawarwari, ki yabe shi, tare da yi masa addu’ar dorewa da kariya.

2-  Ki san bangarorin da yake da rauni a cikinsu domin ki taya shi magance su. Kar ki ingiza mai kantu cikin ruwan mutuwar jiki da kasala da cutar son duniya.

3-  Daga himmar mai gidanki sama, ki taimaka masa ya shiga cikin – ko ma gaba-gaban – masu rige-rige cikin ayyukan alheri, ya zama mai amfanarwa ne ga al’ummar Annabi (s.a.w).

A karshe, kar ki manta cewa: Allah ba ya tozarta duk wani kokarin mai kokari ko mai kankantarsa. Allah ya ce: Tashi in taimake ka! Saboda haka kada ki rena duk wata dama da kika samu cikin alheri. Ko ya motsi yake ya fi labewa.

Nafisatu Abubakar (Umm Abdallah)

Published in: on at 11:33 am Leave a Comment

Ladubban yin Sulhu Tsakanin Masu Gaba

Gaba tsakanin musulmi babban zunubi ne; domin Allah ya wajabtawa musulmi son juna da kyautata wa juna, shi ya sa gusar da wannan zunubi ta hanyar yin sulhu tsakanin masu gaba ya zamo ibada ce da Allah yake so. Ga wasu ladaddakin wanda ya aikata wannan alheri.

1- Rabauta da rahamar Allah: Allah Ta’ala yana cewa a cikin ma’anar wata aya: ((Hakika muminai ‘yan uwan juna ne ; saboda haka ku sulhunta tsakanin ‘yan uwanku, ku kuma ji tsoron Allah domin ya rahamshe ku)) (Hujurat: 10).

2- Samun soyayyar Allah ; domin duk wanda ya kyautatawa ‘yan uwansa Allah yana son sa kamar yadda ya ce a ma’anar wata aya: ((Ku kyautata, domin kuwa Allah yana son masu kyautawa)). (Bakara: 195). Sulhu kuwa kyautatawa ne ga ‘yan uwa musulmi.

3- Samun ladan yaye wa musulmi matsala da gusar musu da wata cuta ; domin tabbas sabani tsakanin musulmi yana dauke da cutar da su duniya da lahira. Allah ya azarta mu da yi masa biyayya da kuma taimakon bayinsa.  

Rabi’atu Aliyu Umar (Umm A’isha).

Published in: on at 11:25 am Leave a Comment

Habaka Son Allah da Manzonsa a Zukatan ‘ya’ya

Habaka son Allah da manzonsa a zukatan yara ba karamin mahimmanci ne da shi ba, don wannan zai sa su rika bin Allah da manzonsa sau-da-kafa, a komai wanda wannan ya hada da biyayya ga iyayensu. Wasu daga cikin hanyoyin dasa wa yara ko habaka kaunar Allah a zukatansu su ne:

1. Iyaye su rika nuna son Allah a mu’amalarsu

2. A rika yi wa yaro bayanin waye

3. Gaya wa yaro ni’imomin da Allah ya yi masa

4. Gayawa yaro cewa komai Allah ne yake bayarwa

5. Gaya yaro kyautar da Allah ya shirya wa mai yi masa biyayya

 Zainab Ibrahim

Published in: on at 11:16 am Leave a Comment

Wa zai Canka!?

Mai kokari kawai nake so ya yi Magana.

Af! Assalamu alikum, shekarata takwas, kuma sunan matar Annabi ta farko ne da ni; Khadija, kuma a Madina aka haife ni, kai  Allah na gode maka!

Ga wasu sunaye guda hudu na wasu manyan mutane a musulunci:

1- Abubakar Saddik.

2- Ali bin Abi Talib.

3- Umar Bin Khattab.

4- Usman bin AffanTambayata a nan ita ce:

  •  Su wanene wadannan mutanen? Annabawa ne ko Sahabbai? Ko malaman makaranta?  
  • Menene taken kowanne? 
  • Na Jera wadannan sunayen gwargwadon harufansu na farko, ku kuma ku jera su gwargwadon daraja da kuma zamanin kowanne daga cikinsu. 
  • Hada kokarin bara da na bana ki nemo amsa. Ina jiran ki Wassalamu alaikum.

Kawarku Khadija Muhd. Muslim

Published in: on at 1:29 am Comments (1)

Kwas na musamman don ‘yan mata

Bangaren matasa da ‘yan mata na wadannan cibiyoyi masu albarka (A1 families da Nana Asma’u Women Center), ya gabatar da kwas na matasa ‘yan mata (Teenage Program) na farko wanda a ka gudanar  daga ranar 30/12/2007 zuwa 01/01/2008.

snapshot03.jpeg  snapshot02.jpeg  snapshot07.jpeg

Manufofin wannan shiri

  • Samar da mata na gari masu imani da Allah da riko da koyarwar addininsu tare da wayewa ta zamani don gyaran al’umma.
  • Sanya ‘yammata a hanyar zama kwararru akan duk abubuwan da suka shafi mata a addininsu da rayuwarsu ta yau da kullum.
  • Dasa tushen samar da rayuwar iyali ingatacciya, ta buga misali.
  • Taimakawa iyaye wajen tarbiyyar ‘ya’yansu da gano irin abubuwan da suka dace da ‘ya’yan don karfafarsu a kai.
  • Gano da kokarin shawo kan matsalolin tarbiyya, alakar ‘ya’ya da iyayensu, da zamantakewar aure tun kafin su bayyana.
  • Samar da bincike da rubuce rubuce a kan hanyoyin tarbiyya da kura-kuran da ke afkuwa cikinta don magance matsalolin da su ke haifarwa a al’umma.

Abubuwan da shirin ya kunsa:

 Shirin ya kunshi laccoci da wasannin kwaikwayo (da harshen Larabci) da kacici-kacici (da harshen Hausa) da kuma mahawara (da harshen Turanci) baya ga horo na musamman a kan amfani da kwamfuta.

Shirin, wanda Mai bawa gwamna shawara a harkar mata, Hajiya Mariya Sanusi Mahadi ta bude, ya samu halartar ‘yan mata sama da 60 kuma dalibai na farko da wadannan cibiyoyi suka fara horaswa (trainers) ne suka gabatar da wannan kwas din gaba dayansa.  

Laccocin da aka gabatar, sun hada da:

  • Kissoshin Magabata Mata – Asma’u Bukhari Safwan,
  • Kula da kai (ko Tsaftar Jiki) – Binta Imam,
  • Lokacin balaga – Hassana Sani Darma,
  • Alaka da maza da Suturar ‘ya mace – Fatima Isma’il,
  • Abubuwa biyar kafin biyar – Hauwa Uba Sa’id
  • Abubuwan da Musulunci ke nema daga Matasa – Jameela Abdul Azeez
  • Jinin Haila da hukunce-hukuncensa – Sadiya Adamu Aliyu

Daga cikin muhimman abubuwan da shirin ya yi akwai jin ra’ayoyi, shawarwari da korafe-korafen yaran da suka shiga shirin da nufin samar da hanyoyin magance su.

Idan a ka ci gaba da bibiyar wannan fili za a samu karin bayani da kuma sakamakon wannan bincike da aka gudanar.

Da yardar Allah, nan gaba kadan, za mu gudanar da wani shiri na musamman don horas da iyayen wadannan yara da sauran iyaye game da hanyoyin tarbiyyar matasa da kuma sanar da su irin abubuwan da ‘ya’yansu ke korafi a kan su domin daukar matakan da su ka dace. 

A karshen wannan kwas din, an rarrabawa matasan kyaututtuka na littattafai, man shafawa, turare, man goge kaushi da sauransu.

Published in: on at 1:25 am Leave a Comment

A Dinga Sara ana duban Bakin Gatari

‘Yar uwa! Kada ki manta da cewa duk mai rai fa zai mutu, kuma kowa zai shiga kabari, kabari kuwa dayan biyu ne, ko dai ya zama gidan ni’ima, gidan dadi da yalwa, kuma a fadadawa dan aljanna kabarinsa gwargwadon zira’i saba’in zai kasance cikin ni’ima har zuwa tashin alkiyama. Ko kuma ya kasance gidan azaba da kunci da wahala, za’a rika yi masa azaba tun daga kabarin ana kuma dukansa da guduma ta wuta. Kuma za’a kuntata masa kabarin a matse shi har kasusuwansa su rika kara, wanda da mutanen duniya za su ji da sun narke saboda tsananin firgita.Bayan kwanciyar kabari na iya shekarun da Allah ya kaddara, za’a tayar da mutane su tashi a firgice cikin dimuwa, kowa yana gudu ba tare da ya san inda ya nufa ba. Sannan a gurfanar da mutane a gaban Allah (SWT) wanda babu wani sarki a wannan ranar sai shi.Laa ilaha illallah! Hakika wannan rana ce ta tonon asiri, ranar tonon silili, ranar da babu abin da zai boyu sai an bayyana shi. Allah muna rokon ka ka kiyaye mu ka fitar da mu daga azaba, da tsoro da firgita na wannan rana, amin.‘Yar uwa bayan wannan hisabi, kowa za’a ba shi masaukinsa da ya dace da ayyukansa a mazauni na dauwama guda biyu; ko dai aljanna wadda fadinta ya kai nisan dake tsakanin sama da kasa. Ko kuma wuta mai tsananin zafi wadda har sashenta yana cinye sashe. Allah ka nisanta mu daga wuta, ka tserar da mu amin. Mai rabo shi zai shiga aljanna, Allah ka sa muna da rabo a cikinta da iyayenmu, da mazajenmu da ‘ya’ya da duk zuriyarmu, da duk musulmi baki daya. Marar rabo kuma wanda ya butulce wa ubangijinsa, ya bi son zuciyarsa, wannan wuta ce makomarsa. Allah (SWT) yana cewa:“Duk wanda ya kubuta daga wuta kuma aka shigar da shi aljanna hakika ya rabauta” (Ali Imran 85).Ya ke ‘yar uwa! Hakika bana shakkar cewa kina kaunar samun wannan babban rabo; don haka kada ki kuskura ki yaudari kanki, ko a yaudare ki, aljanna ta wadanda suka yi aikin kwarai ce, yin imani da ayyuka na kwarai su suke isar da mutum kofofin aljanna, kuma karantar Alkur’ani shi ne tsanin da ake hawa benayen aljanna.Saboda haka ‘yar uwa, ki nisanci duk wasu shaidanu da na ambata miki ire iren su a baya wadanda a ko yaushe suke son su ga kin yi wa Allah tawaye ki bata, kuma ki halaka. Ki toshe kunnuwanki daga duk wani kiran ‘yanci ko hudubar shaidan da za su rada miki, ki ce musu Ahir dinku.Ki zama baiwar Allah ta gari, mai tarbiyyantar da ‘ya’ya na gari wadanda za su zama manyan gobe. Ki zama babban jigo na gina wannan al’umma, kada ki zama hanyar ruguza ta.A karshe nake kara jaddada mana cewa yin riko da Alkur’ani da sunna shi ne zai kai mu ga gaci muddin mun rike su ba za mu bata ba, ba kuma za mu tozarta ba, a nan duniya, kuma a lahira mu samu sakamako mai girma. Allah ya sa mu dace Amin.Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka bamu ikon bin ta, muyi aiki da ita,  Ka nuna mana karya Ka ba mu ikon guje mata. Allah Ka ba mu aljanna don rahamarKa, Ka nisantar da mu daga wuta. Allah Ka jikan iyayenmu da kakanninmu da ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu, da duk musulmi baki daya. Allah Ka yafe mana kura-kuran mu Amin. 

Safiyyah Hussain Falaki

Published in: on at 1:19 am Leave a Comment

Wasiyyar Abil Walidil Baji ga ‘ya’yansa

Abu walid Albaji wani bijimin malami da ya rayu a karni na biyar ya yi wa ‘ya’yansa wata mahimmiyar wasiyya da ya kamata duk wani uba da malamin makaranta ya nazarinta, ya kuma amfana da ita wurin tarbiyyar ‘ya’yansa ko dalibansa.

Bara in dan tsakurowa mai karatu wani abu daga cikin wannan hamshakiyar wasiyya. 

  1. Ku kiyaye dokokin Allah a fili da boye.
  2. Ku kiyayi gina wani hukunci akan ilimin taurari, ko bokanci, domin wannan fitar da wanda ya gasgata shi yake yi daga addni, ya kuma shigar da shi cikin kangararru 
  3. Ba ku ba zulunci,  girman- kai,  hassada, gulma da munafunci 
  4.  Ku guji sauraron kade-kade; fitina yake haifarwa a zuci, da tunanin aikata sabo 
  5.  Kada dayanku ya fifita wani abin duniya akan danuwansa, sai ya rika yiwa danuwan nasa rowa saboda shi, ko ya juya masa baya, ko ya rika gasa da shi a ciki. Wanda Allah ya yi wa arzuki a cikinku to su ci tare da danuwansa, kar ya kadaita da shi, ya yi kokarin habaka dukiyar danuwansa, kamar yadda zai yi kokarin habaka tasa… ‘Yaruwa salon wasiyya salo ne na Annabawa da nagartattun bayi  a tarbiyya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda kike tsammani,  gwada shi ki ga bambanci. Allah ya sa mu dace  

 Batulu Aminu Dantata 

Published in: on at 1:04 am Leave a Comment

“Tufka da Warwara”

An karbo Hadisi daga Abu Huraira Allah ya kara yarda da shi ya ce:        

An tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa:  Ya Rasulallah! hakika (wance) tana sallar dare, ta yi azumin nafila da rana, tana aikata ayyukan alkhairi, kuma tana sadaka, amma tana cutar da Makotanta (da harshenta)! Sai ya ce: “Babu alkhairi a gareta tana daga cikin ‘yan wuta” sannan aka ce (wance) kuma tana salloli wajibabbu, ta yi sadaka da dan abu kadan, amma bata cutar da kowa. Sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ita yar aljanna ce”. (Bukhari fil adabil mufrad).

‘YAR UWA IDAN KIKA DUBA WANNAN HADISI ZA KI GA CEWA DUK ALKHAIRIN DA KIKA KULLA TO CUTAR KISHIYA YA WARWARE SHI. WANNAN SHI NE TUFKA DA WARWARA. ALLAH YA YA KIYAYE AMIN.

Ummu Huwailat

Jamilat Bint Abdul’Aziz Alkazauriyya. 

Published in: on at 12:16 am Leave a Comment

Hankoron jijjige matsala Ya kai ga karyar Cutar jijjiga!

Wasu matan suna da ragon azanci wurin magance masalar da suka samu kansu a ciki, sai su yi gudun gara su tarar da zago, ko su debo ruwan dafa kansu, ko su janyowa kansa abin fada har abada ana ganinsu da abin.  

Haka ce ta sa na yi tunanin fadakar da ‘yanuwana bisa wannan susanci da wasu mata kan fada ciki.  A wani lokaci ‘yan shekarun baya, a asibitin Murtala na Kano, bangaren ‘yan haihuwa, dakin ‘yan jijjiga, wani labara ya faru abin takaici, abin haushi, kuma abin dariya duk a lokaci guda. Wata rana ce wani mutum ya zo da matarsa a asibiti a demauce ita da   ‘yanuwanta kamar a sussume, suka ce jijjiga take yi.        

Ganin cewa matar kwana guda kenan da haihuwarta, sai ga unguwar zomar (mid wife) ta karbe ta ta kwantar da ita da nufin ta auna ta don ta tanadi bayanin da likita zai bukata game da ita Da unguwar zoman ta dauko abin awon jini wato (Blood pressure) to ba sai ta ga mata ta runtse idanunta ba, amma kuma tana ta karkada kafadunta da hannayenta ita wai ba ta yarda ba jijjiga take yi!Da unguwar zoman ta fahimci dawan garin,  sai ta ce: “duk wadanda suka kawo ta su kauce su ba da wuri” Sai suka kama gardama suna cewa: ai in sun bar ta ita kadai za ta fado. Duk sun gama gigicewa.Ita kuma ta tsaya kai da fata sai sun ba su wuri. Da kyar dai suka hakura suka fita.

Bayan sun ba su wuri sai ta ce da ita: “Haihuwa!!!” dan daure ki bar min wannan hannun don na auna ki amma kina iya girgiza waccan!

Abinki da rashin sani, gaular taki sai kawai ta bi umarnin; Ta canza hannun da take girgizawa! Wai ita za’a auna ta, sannan kuma ko karaya ta yi, sai ta dan bude idonta kadan don ta fahimci me ake son ayi mata. 

Da unguwar zoman ta fahimci haka, sai ta kirawo mijin wanda yake cikin mummunan tashin hankali ta tambaye shi, ko waani abu ya faru a tsakaninsu?

Da yake baya son fadan sirrinsa. Sai ya ce ai malama kin san ita rayuwa ba’a  rabuwa da ‘yan matsaloli!  

To a nan ta fede masa biri har wutsiya, ta ba shi tabbacin cewa matarsa lafiyarta lau, cutarta ta matsaloli ce ba ta rashin lafiya ba! sai dai da hadin kansa za’a bar ta a asibiti ta yini, ta nutsu, sannan a sallame ta. Ita kuma matar daga bisani aka ja hankalinta cewa nan gaba ba haka ake nuna fushi ba, ta yi kokarin warware matsalar tare da mijinta a gida ba sai ta yi abin da za’a kawo ta asibiti ba don hadarin da zai iya shigar da ita.Allah ya kyauta.

Sadiya Adamu Aliyu       

Published in: on at 12:05 am Leave a Comment