Imamu Shafi’i lokacin yana dan Yaro

Assalmu alaikum abokaina na Najeriya da na Madina,

Kun kuwa san yadda imamush shafi’a yake lokacin yana dan yaro?

To zan gaya muku, amma kafin nan barain fara gaya muku wanene shi ma tukuna IMAM ASSHAFI’I, sunansa (MUHAMMAD BIN IDRIS) Wani babban malami ne da aka Haifa a garin “Gazza”, wanda yake a Kasar “Palastine” -inda a yau yahudawa kullum suke kashe musulmi- a shekara ta (150) bayan hijira, ko da yake iyayensa mutanen Makka ne, kuma ‘yan Kabilar Kuraishawa ne, Kabilar Manzon Allah (s.a.w).

Ya nemi ilimi a wurin malamai masu yawa, a garuruwa daban – daban, musamman Makka da Madina. Daga cikin manyan malamansa da akwai Imamuna Maliku.Iliminsa ya kai ya kawo, ya tumbatsa har ya kafa mazahaba wadda ta zama daya daga cikin manyan mazahabobin Ahlussunnah wal jama’a guda hudu. Ya kuma rubuta littattafai masu yawa. Ga shi da yawan ibada, kullum sai ya yi sallar dare, ga shi da tawalu’u matuka da gaske, ba ya ganin kansa komai! Har Allah ya dauki ransa a shekara ta (204) bayan hijirar Manzon Allah (s.a.w).

Allah ya jikansa ya amfane mu da ilimummukansa.

Imamu shafi’i tun yana dan yaro an ce himma ce da shi kamar me, ga basira da hazaka, ga ladabi da biyayya, duk inda aka aike shi nan da nan zai yi sauri ya dawo, Babarsa tana son sa sosai saboda kirkinsa da kokarinsa. Ni dai Imamush Shafi’i yana burge ni, in sha Allahu sai na zama irinsa, na san kuma kuna so, to sai mu dage, kuma muce baban ninmu su rika yi mana addu’a.

Abdallah Muhd. Muslim (shekara 12).

Published in:  on February 8, 2008 at 3:39 am Leave a Comment

The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2008/02/08/imamu-shafii-lokacin-yana-dan-yaro/trackback/

RSS feed for comments on this post.

Leave a Comment