Kula Kulan Jifan Yunwa (Dan wake)

Dan wake daya ne daga cikin tarin abinciccikan gargajiya na  hausawa, saboda yadda yake yi wa yunwa rajamu ake yi masa take da “Kula kulan jifan yunwa

Yadda ake yin danwake:

1.     Farko dai za’a jika kanwa.

2.     Sannan a  samu garin fulawa, ko garin rogon dan wake a tankade

3.     Sai a tankade kuka ‘yar madaidaiciya a hada da wannanan tankadadden garin a tona su gaba daya

4.     Sai kuma a kawo waccan  jikakkiyar kanwa  a zuba a kai

5.     Sai a yi ta tonawa har sai ya hadu.

6.     Sannan a samu tukunya mai kyau a zuba ruwa a dora akan wuta har sai ya tafasa

7.     Sai a rinka diban wancen kwababben kulun ana gutsurar dai dai gwargwadon yadda ake so ana jefawa cikin wannan tafasashen ruwan

8.     Idan aka gama sai a bar shi ya yi ta tafasa, ana yi ana juyawa, a ba shi dan lokaci kadan

9.     Daga nan sai a rika tsamewa ana zubawa cikin wani ruwan daban mai sanyi ko mai dumi.

10.  Sannan  a samu abin suya a zuba mai – na na kuli, ko na ja-  sai a yanka yar albasa a ciki a soya 

11.Idan ya soyu sai a kwashe

12.Tuni dama an an tanadi dakakken yaji mara daddawa (mai fada, ko mara fada)

13.Sai a kwashe wannan danwaken, a tsane shi, sannan a zuba shi a kwano wankakke

14.Sannan a bade shi da yajin nan, kuma a dan bar bada gishiri, ko a marmasa magi

15.Daga nan kuma sai a zuba wannan soyayyen man

shaikenan danwake ya hadu, sai ci, amma kar a manta bisa al’ada shi dan wake hakkinsa shi ne a ci shi da tsinke ba da cokali ba, a ci lafiya, amma kar a manta da hankicin share gumi.

Hajiya Binta Lawan (Umma Imam) blabdallah@yahoo.com

Published in:  on February 7, 2008 at 9:10 pm Leave a Comment

The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2008/02/07/kula-kulan-jifan-yunwa-dan-wake/trackback/

RSS feed for comments on this post.

Leave a Comment