Da sunan
Allah mai tarin raham
a da yawan jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga mafi daukakar annabawa da manzanni; Annabi Muhammadu (SAW)
Bayan haka zan yi amfani da wannan kofa domin jan hankalin ‘yan uwana ‘yan mata matasa game mahimmancin lokaci, da kiyaye shi. Ya ‘yar uwa hakika yana da matukar kyau ki san kimar lokacin da Allah (swt) ya tanadar gareki, haka nan ki san yadda za ki yi tattalinsa; domin ki amfani kanki da al’ummarki da shi ki nemi guzirin tafiya lahira, kar ki zauna ki shantake kina sharholiya, da karance-karance marasa amfani, ko kallon fina-finai, ko hotuna masu nuna tsiraici, ko tunane-tunane marasa kan-gado, ko maganganu wadanda ba su kamata ba. Wadannan duk ba za su amfane ki da komai ba, sai dai su kara dilmiyar dake a cikin halaka, da jawo miki da-na-sani.
Ki tuna lokaci ba ya jiran kowa.!Yi kokari ki ga kin amfana da lokacin da kike da shi, ki kasance a koda- yaushe cikin
· Ambaton Allah, da
· Yin kowace sallah akan lokaci,
· Yawaita yin Nafilfili,
· Yawaita karatun Alqur’ani
· Karanta littatattafai na ilimi da zaki karu,
· Sauranron kasa-kasai na wa’azi ko lacca wadanda za ki amafana da su duniya da lahira, · Yin zikirin safiya da maraice wadanda ake kira (Alma’athurat) da makamantansu.
· Taya mahaifanki aiki a gida kamar girki, shara, yi wa kanne wanka dssMatukar kin kiyaye wadannan abubuwa, da shauran ayyuka na alheri da ban zayyana ba, ina mai yi miki albishir da in sha Allah za ki kasance cikin rayuwa ta jin dadi da samun biyan bukata, da samun kusanci da Allah (swt) tare da samun yardarsa, da samun karin kaunar iyaye da yardarsu, kuma ki rika jin cewa kina da amfani a wannan rayuwa, ba ‘yar rakiyar zuwa duniya b ace. Don haka sai ki kiyaye, ki guji zaman bata lokaci, ki zauna kurum ba tare da kin yi amfani kanki da wani abu ba; domin wannan shi zai kara jawo miki abin da zai cutar dake, da jawo miki wasu-wasi, da bacin rai da shakka. Saboda haka, nake gargadin ‘yan uwana matasa da su dage da yin addu’a kowane halin da suka sami kansu da su yawaita karanta wannan addu’a: “ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI WA A’UZU BIKA MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI, WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA QAHRIRRIJALI” Idan har kina yawaita karanta wannan addu’a da bibiyar ma’anarta, insha’Allahu, Allah (s.w.t) zai ya ye miki damuwarki, da bakin ciki, ko bacin rai.
Ya ‘yar uwa ta! Ya kamata a kowane lokaci ki kasance cikin shiri da tanadi domin wannan rana mai zuwa (Alkiyama). Kuma kada ki damu da wani abu na rayuwar duniya wanda ba tabbatacce ba, har ranki ya rinka baci akansa don baki same shi ba kiyi hakuri, hakika Allah yana tare da masu hakuri, kuma lallai babu wani tabbataccen abu sai aikin mutum na kwarai.Allah (s.w.t) yana cewa: “wanda ya yi aiki na gari daga cikinku, namiji ko mace zamu raya shi rayuwa mai dadi, kuma zamu saka musu da mafi kyon abin da suka aikata”(Suratun-nahli)Allah yasa mu dace Amin
MARYAM JAMILA MUHAMMAD