Menene Sirrin NASARATA a karatun Boko?

‘Yan uwana matasa Assalamu alaikum.Ina yi wa Allah Ta’ala godiya bisa ni’momin da ya yi min ba iyaka, wadda daga cikinsu akwai kokari da hazaka a makaranta, har ya zamana bayan saurin fahimtar karatu da nake yi, in dai za a yi jarrabawa, to kuwa in sha Allahu ni ce zan yi ta daya,  sai dai kuma  wani ikon Allah, wannan ya sa nake jin dadin rayuwata ta makarnata, saboda kullum iyayena suna farin-ciki da ni, suna kara sona, sannan ga farin-jini da nake da shi cikin kawaye, saboda wannan hasken na karatu da Allah ya ba ni. 

Wata rana wata kawata ta tambaye ni: “Ke kuwa me ya sa kullum kike sahun gaba wurin fahimtar  karatu, da cin jarrabawa?”

Na yi tunani mai zurfi, sai na ga bayan taufiqi na Allah, da tsayuwar iyayena akaina HADDAR ALQUR’ANI MAI GIRMA tana daga cikin manyan dalilalai na samun wannan gagarumar nasara. Wasu bincike-bincike da aka yi na ilimi a Saudiyya sun nuna cewa daliban da suka samu kula ta musamman game da Alqur’ani tun suna yara, suna bai wa takwarorunsu da ba su samu wannan kulawar ba tazara a fahimtar ilimummuka na zamani, da rata mai tarin yawa a jarrawa.

Sannan na ji an ce Dr. Bashir Galadanci- mai bai wa gwamnan jaharmu shawara akan ilimi da kimiyya- ya ce: tun da yake  bai taba ganin daliban da suka fi alarammomi saurin gane kumfuta ba a cikin daliban da ya taba koyarwa.

Don haka nake bai wa ‘yanuwana matasa musamman mata da su dage da karatun Alqur’ani, da haddace shi, wannan zai kara musu basira da kwakwalwa da nasara a jarrabawa, kamar yadda nake bai wa iyayenmu shawara da su kara dagewa wurin ganin ‘ya’yansu sun samu rabonsu a Kura’ni kafin lokaci ya kure, musamman da yake Koyar da yara karatun Alqur’ani tushe ne babba daga manyan tuwasan musulunci; Ibn Taimiyya Allah ya jikansa ya ce: “Haddar Alqur’ani ita ce abin gabatarwa akan duk wani ilimi”  

Baya ga wannan kuma, ga tarin fa’idojin da haddar Kur’anin ta kunsa kamar:

1.  Samun budi a karatun zamani kamar yadda na fada a baya.

2.  Kasancewar Alqur’ani zai yi ceto ga ma’abotansa ranar Alkiyama kamar yadda manzo (s.a.w) ya ce: “Ku karanta Alqur’ani; domin zai yi ceto ranar alkiyama ga ma’abotansa ” (muslim).

3.  Mahaddacinsa zai sami daukaka a duniya da lahira.

4.  Wanda ya haddace shi zai zama daga cikin zababbun wannan alumma, saboda fadin manzo (s.a.w): “mafificinku shi ne wanda ya koyi karatun Alqur’ani kuma ya koyar da shi” (Bukhari).

5.  Samun lada mai yawa wurin karatunsa, kamar yadda Annabi (s.a.w) ya ce: “wanda ya karanta  harafi daya na Alqur’ani, yana da aikin lada daya, aikin lada daya kuma yana da lada goma ……… ” (Tirmizi)

6.  Iyayen da suka tsaya tsayin daka akan karatun ‘ya ‘yansu na Alqur’ani suna da lada mai yawa da babban sakamako a wurin Allah.

Alqur’ani littafi ne – duk da cewa yana da yawa- amma saukin hadda gareshi; saboda Allah ya sauwake haddarsa kamar yadda ya zo a suratul Qamar, kuma kamar yadda haddar tasa a aikace ta tabbar; don haka ‘yan uwana matasa kada ku yi kasa a gwiwa wurin dukufa wurin haddace Alqur’ani mai girma, musamman a wannan zamanin da haddar tasa ta kara sauki; saboda yaduwar makarantun hadda na zamani, da kuma na’urori daban daban na na kimiyya, kamar irin su kaset da rikoda, kumfuta, wayar salola dss, baya ga makarantun Allo da tsangayoyi da suka dade suna ba da gudun mawa a wannan fage; don haka kada wata ta ce: “Ga bikin zuwa babu zani” sai dai ta ce: “In ba ki yi ba ni wuri“!

A karshe ina godiya ga mahallicina  Allah da ya albarkace ni da haddace littafinsa mai girma, haka nan ina godiya ga makarantar Darul Arqam ta Kano wadda a cikinta ne na samu wannan haske, Allah ya ja zamaninta, ya kara mata daukaka, ya kuma taimaki shuwagabanninta da malamanta, ya kuma saka musu da alheri.

Kamar yadda nake mika godiya ta musamman ga babbar yayata da mijinta wadanda suke matsayin iyayena, don jajircewarsu da kulawarsu, da addu’arsu ne suka sa na samu, hada da tabbatuwar wannan haske na Kur’ani a zuciyata, Allah ya albarkanci rayuwarsu, ya ba su tsawon rai cikin bautar Allah,  koshin lafiya  da alheri, ya kuma saka musu da jannatul Firdausi ranar gobe Kiyama. Amin.

FATIMA HUSAIN FALAKI

Published in: on February 6, 2008 at 11:21 pm Comments (2)

Tambaya ta 0001

Tambaya: Idan mace mai haila ta yi tsarki sai ta yi wanka bayan sallar asuba ta yi sallah kuma ta dauki azumin wannan ranar, shin za ta rama ko azuminta ya yi?

Amsa: Idan mace mai haila ta yi  tsarki kafin fitowar alfijir ko da da minti daya ne, amma dai ta tabbatar da tsarki, idan har a cikin Ramadan ne, to wajibi ne gare ta ta dauki azumi. kuma azuminta ya inganta ba sai ta rama ba,  domin ta yi azumi ne a cikin tsarki ko da kuwa ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar yadda namiji idan janaba ta same shi ta hanyar jima’i ko mafarki, yake sahur ya dauki azumi, alhali bai yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir kuma azumin sa ingantacce ne.Dangane da wannan, ina so in fadakar da mata game da wani al`amari shi ne idan haila ta zo wa mace, alhali ta yi azumin wannan rana; wasu mata suna zaton cewa, idan haila ta zo bayan an sha ruwa kafin ta ci wani abu, ko kuma bayan faduwar rana da kankanin lokaci cewa azumin ta ya karye. A`a azuminta yana nan, kuma ingantacce ne (ba sai ta rama ba).

Sheik Muhammad Sahel Al-Uthaimeen

Published in: on at 11:11 pm Leave a Comment

Ya saki mata BIYAR Lokaci Guda!

Wani mai gida ne ya dawo a fusace, Magana ba Magana ba sai ya ce ya saki uwar gidansa! to ita kuma tana zaman arzuki da abokan zamanta guda uku, sai ta biyun  tasu hankalinta a tashe ta ce mai gida yau kuma me zan gani!, sai ya ce ke ma na sake ki!, ta uku ta taso a sukwane,  ta ce haba mai gida a rika hakuri! sai ya ce ke ma na sake ki! Ta hudun ta zo tana kuka ta ce mai gida yanzu ka saki mata uku lokaci guda! Amarcin matan nan bai cece ta ba, kwai sai ya ce ke ma ki bi su na sake ki!  Haba ba  sai gida ya rude da kuka ba. Makociyarsu ta kasa hakuri ta shigo gidan, musamman da yake ba’a saba jin irin wannan koke-koke ba, ta dauka ma mutuwa aka yi, bayan ta fahimci abin da ya faru, sai ta ce: haba baban wane a rika abu da hankali mana! Sai  rufe min baki,  ke ma in mijinki ya dawo in dai ya yarda ki tafi gidanku na sake ki!!! Illar fushi kenan, me  ka sani na koyarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam game da wanda ya samu kansa a cikin fushi???  In ba ka sani ba, tambayi malamai.

Published in: on at 11:00 pm Leave a Comment