Addu’a makamin mumina

Assalamu Alaikum Warahmatullah

‘Yar uwa a musulunci, hakika Addu’a tana da tasiri a rayuwarmu, musamman mata.

Yar uwata, Addu’a fa karki manta ita kanta ibada ce domin Allah (S.W.T) yace: “ku roke Ni zan amsa muku” suratu gafir.

Don haka duk abin ya same ki ‘yar uwa gaya wa Allah. sai  ki sami maganin matsalar ki.

Sannan Annabi (S.A.W) ya ce: (Addu’a makamin mumini ce) kin ga ashe ba ki da wani abin kamawa wanda ya wuce Addu’a.Allah ya sa mu dace Amin.                       

Asma’u Bukhari Safwan

Published in: on February 21, 2008 at 8:02 pm Leave a Comment

Humra

Humra turare ne wanda aka samo asalinsa daga Arabs, (Larabawa) kuma Bare-bari suka dauka a matsayin kwaikwayon al’aadar, sannan ta  yadu a kasar Hausa, kusan duk mata sun karbe shi  sakamakon irin ingancinsa tare da cikakken muhimmmancinsa. Turaren Humra na dauke da sinadarai masu kamshi, ana kuma hada shi ne da saiwoyi da nau’oin turarruka daban-daban, kuma ta kan zo a nau’in bakar humra ko fara har ma da koriya.

Abubuwan da ake hada bakar Humra da su

Ruwan turare (Alchohol) litre 1

Madarar turare 1/6 litre

Ambir 4 (gwayar shi)

Garin sandal cb 2

Garin Humra cb 3

Garin soyayyen kaninfari ck1

Mahalan (gari)  ck 1/2

Yadda ake hada bakar Humra:

1.   Za’a sami ruwan turare a zuba masa nikakken ambir

2.   Sai a kawo garin nikakken tankadadden sandal da garin Humra da soyayyen garin kaninfari, da garin mahalan, a zuba a hada su a girgiza, a kawo madarar turare irin nau’in da ake bukata a zuba, zai iya kasancewa fiye da daya ko fiye idan sun hadu sai a zuba a cikin kwalabar turare a rufe.

Farar Humra da Koriya

Ita ba’a sa mata garin Humra, shi ne kadai babu, a cikin koriyar Humra kuma kala ake sa wa koriya, ita ma din kadan, kuma babu garin Humra a cikinsa. Wannan kawai shi ne bambanci tsakaninsu.

Hajiya Binta Imam                                        

Published in: on February 17, 2008 at 12:44 pm Leave a Comment

Don kar Mage ta Cinye!

Shehu Jaha ya saba kullum ya sayo gari, ganyaye (na ci) da kuma kayan marmari ya kawo gida, ita kuma matarsa ta saba ta dafa ganyayen, kayan marmarin kuma ta aika wa kwarta kyauta!

Kullum dare idan Jaha ya hakimci don ya kwashi girki da kayan marmari, ba abin da matar nan take kawo masa sai gurasa tsura!

Abin dai yana ta daurewa Jaha kai.

Rannan dai sai ya yi ta maza; ya tsaga bullensa ya tambayi matar:

“Wai ni ina ganyaye da kayan marmarin da nake shigowa da su kullum; ina kike kai su?” Sai matar ta kada baki ta ce:

“Abin da ka samu ka godewa Allah wannan shi ne rabonka!!! duk lokacin da na dafa wani abu MAGE take cinyewa”

Jaha ya dan tsaya tsai yana tunani akan maganarta, sannan sai ya yi wuf ya zabura ya dauke GATARINSA da yake rataye a jikin garu ya wurga shi  cikin akwati ya garkame.  

Sai matar ta tambaye shi:

“Jaha lafiya menene na buye gatari kuma?”

Sai ya ce:

“Na boye shi ne don kada mage ta gani ta cinye!

Sai matar  ta cika da mamaki, har ta yi wata irin shewa ta ce:

“Mahaukaci ne kai! Mage tana cin gatari ne!!

Sai Jaha ya ce mata:“Wallahi da hankalina sarai, amma ke me kike gani; yanzu magen da za ta rika cinye girkin dirhami goma, da kayan marmari na dirhami goman (ashirin kenan), INA GA GATARIN DIRHAMI UKU!!?”

Published in: on February 16, 2008 at 5:36 am Leave a Comment

Me Za ki Iya yi a Minti Daya?

‘Yar uwa musulma, hakika ya kamata ki sani cewa lokaci yana da matukar muhimmanci; bai kamata ki sake ki yi asarar ko da minti daya, ke ko dai dai  da sakan daya ba ma ba tare da kin aikata wani abin da zai amfane ki ba a cikin sa.

Na jarraba naga cewa cikin minti daya zaki iya aikata alhairai masu yawa.

Safiya Husain Falaki

Published in: on February 12, 2008 at 10:43 pm Leave a Comment

“Ko Uwaka Za ka yi”!?

Wata rana wani baywan Allah zai shiga ban-daki, sai wani dan karamin dansa ya tambaye shi:

“BABA ME ZA KA YI?”

Sai ya yi masa banza, to kin san yara da tambaya, sai ya kara tambayarsa

“BABA ME ZA KA YI?” 

Ya kuma yin shakulatin bangaro da shi, kamar dutse yake yi wa Magana.

Yaron nan dai bai hakura ba sai ya kara tambayarsa. “Baba me za ka yi”

Sai uban ya ka da baki ya ce: “UWAKA ZAN YI!” 

shike nan Magana ta fuce kamar yaro ya manta, wata rana babansa ya yi baki, ta kuma kamawa zai shiga ban-daki, sai yaron nan ya kuma yi masa irin waccen tambaya; “BABA ME ZA KA YI?” shi kuma uban sai ya yi masa banza, shi kuwa yaron sai ya kada baki ya ce: “KO UWAKA ZA KA YI?!”

Sai duk kunya ta kama mahaifin nasa a cikin jama’a.

DON HAKA a tarbiyya yana da kyau duk irin tambayar da yaro ya yi a ba shi amsa, kuma lallai ne a ba shi amsa ta gaskiya, kar a yi masa karya, kamar yadda wasu suke yi in yara sun  tambaye su, ko dai su hana su tambayar, ko su yi musu shiru, ko ma su gilla musu karya, sai bayan sun girma su yi ta kallonsu da abin.

Kamar idan sun ce musu ina kakarsu da ta mutu? sai a ce ta tafi unguwa za ta dawo!

Ko ta ina ake haihuwa? Sai a ce masa ta baki! dss 

Published in: on February 11, 2008 at 8:45 pm Leave a Comment

KISHI

  • KISHI gishirin soyayya idan ya yi yawa ya baci; a dinga cizawa ana busawa.
  • KISHI kumallon mata idan ya taso miki ‘yar uwa ci gauta, ko lemon tsami, ko goro, ma’ana a nan ita ce  ki dinga HAKURI; in mutum ya yi hakuri sai ya dafa dutse ya sha romonsa, hakika Allah yana tare da masu hakuri.

                                                                 Gambo Shehu

Published in: on at 8:32 pm Leave a Comment

SHAYE-SHAYE TSAKANIN MATASA MAZA DA MATA

Ma’anar Shaye Shaye 

Duk lokacin da aka yi maganar shaye-shaye, ana nufin hadiyar kwayoyi masu sa maye ko ganyayyakin da shakarsu, ko cinsu kan fitar da mutum daga cikin tunani irin na ‘yan adam ya koma na dabbobi, Ko sheka wulakantattun abubuwa da mutumin kwarai bazai taba tunawa da suba a wajen abubuwa masu bugarwa da sa maye kamar:

1.     kwatami

2. solution

3. zargina

4. ganyen shayi

5. kashin kadangaru

6. maganin tari na yara dss.(Benelin)

SHIN ME YA JEFA YARAN MU CIKIN IRIN WANNAN?     

Ma iya cewa dalilai ne guda hudu ko biyar.

1.     kwaikwayon miyagun dabi’u ta hanyar kallon fina-finai ko tashoshin ketare ta hanyar gizo da sauran hanyoyin sadarwa.

2.     karance-karancen mujallun batsa marassa amfani

3.     watsi da tarbiyyar ‘ya ‘ya a sakarwa mata ko dan maraici a rasa mai dauka daga cikin dangin, ko rabuwa

4.     yawon almajiranci, tallace-tallace, da aikatau na kananan yara daga karkara zuwa birane.

5.     nunawa yaro gata don iyayensa na da wadata wadannan hanyoyi kowacce na iya jefa yara a cikin mummunar dabiar da zata iya gurbata tarbiyyar su.

To, tunda a zahiri ga shi an san dalilan gurbatar tarbiyyar, menene abin yi don a sami mafita?

LUBANA MUKHAR UMAR  

Published in: on February 10, 2008 at 4:32 pm Comments (1)

TSOTSON HANNU

Menene Tsotson Hannu?

Tsotson Hannu shi ne sanya dan-yatsa da yara suke yi a bakinsu suna tsotsa.

Jarirai da yara sukan sa babban dan yatsa, ko yatsu guda biyu a bakinsu suna tsotsa.

Me yasa suke tsotsan hannu?

  • Tsotson wani abu ne da ya zama wajibi a wurin yaro, don ta haka ne zai ci abinci kuma ya rayu.
  • Duk jaririn da bai samu biyan bukatar tsotsansa ta hanyar ciyarwa ba, to zai tsotsi ‘yan yatsun sa.
  • Tsotson hannu yana sa yaro ya samu gamsuwa ta wani dan lokaci.
  • Tsotson hannu yana ba wa yaro damar kama kansa; wato maimakon ya yi kuka sai ya jefa dan yatsansa a baki ya yi ta tsotsa.
  • Tsotsan hannu ya na kwantar sa hankalin yaro. 

ILLOLIN TSOTSON HANNU

Dr. Hasana Sani Darma 

Published in: on at 4:18 pm Leave a Comment

“Me ya hada ni da Matar wani!”

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude ya saki matarsa, kafin ta gama idda sai wasu suka zo takanas suka tambaye shi Me ya hada ku da wance ne har ka sake ta?

Sai ya ce: “

Mai hankali ba ya tona asirin matarsa”

Bayan ta gama iddar-ke nan ta fita daga hannunsa- sai suka kuma yi masa waccan tambayar dai, sai ya ce:

“Me ya hada ni da matar wani!”

Me ake koya a wannan kissa?

Published in: on February 9, 2008 at 12:46 pm Leave a Comment

MATA IYAYEN GIJI!

Babu kokwanto cewa duk wanda Allah ya daukaka a addini ko a duniya to da akwai sa hannunmu mu mata, ko ta hanyar tarbiya a matsayin uwaye, ko kuma karfafa guiwa da taimako a matsayin mai daki. Ga wasu ‘yan shawarwari domin karfafa guiwar mai gidanki har hakansa ya cimma ruwa ya sami yardar Allah a gidan aljanna.

1-  Ki san bangaren da mai gidanki yake da wata baiwa, kwarewa … domin ki  karfafe shi, ki ba shi shawarwari, ki yabe shi, tare da yi masa addu’ar dorewa da kariya.

2-  Ki san bangarorin da yake da rauni a cikinsu domin ki taya shi magance su. Kar ki ingiza mai kantu cikin ruwan mutuwar jiki da kasala da cutar son duniya.

3-  Daga himmar mai gidanki sama, ki taimaka masa ya shiga cikin – ko ma gaba-gaban – masu rige-rige cikin ayyukan alheri, ya zama mai amfanarwa ne ga al’ummar Annabi (s.a.w).

A karshe, kar ki manta cewa: Allah ba ya tozarta duk wani kokarin mai kokari ko mai kankantarsa. Allah ya ce: Tashi in taimake ka! Saboda haka kada ki rena duk wata dama da kika samu cikin alheri. Ko ya motsi yake ya fi labewa.

Nafisatu Abubakar (Umm Abdallah)

Published in: on at 11:33 am Leave a Comment