02.04.10

Dan tsintuwa a filin Arfa!

Posted in Uncategorized at 8:17 pm by iyalina

Allah madaukakin sarki yana fifita wasu kwanaki, watanni, gurare, lokuta, yanayi, zamani… dss. akan wasu. Hadisi ya inganta daga manzon Allah (SAW) cewa babu wata rana da Allah (SAW) yake ’yanta bayinSa daga wuta zuwa Aljanna irin ranar Arfa, shi ya sa malamai suka ce ranar Arfa ita ce ranar da ta fi kowacce daraja a ranakun shekara, kamar yadda ranar Juma’a take sama da kowace rana a ranakun sati. Hakanan Annabi (SAW) ya bayyana cewa mafificiyar addu’a ita ce addu’ar ranar Arfa…” wannan ta sa za ka ga alhazai sama da milyan  biyu kowa ya dukufa yana ta addu’a ba kakkautawa, kowa yana mayar da hankali akan bukatar da ta fi damunsa, wani ma saboda wannan bukata ya zo haji musamman don ya roki Allah biya masa ita. Amma dai kusan kowa yakan yi kokari ya roki alherin duniya da na lahira. Abin tausayi, abin takaici, daya daga cikin alhazai wanda asalinsa dan tsuntuwa ne (wato dan zina)

Wata rana shi da abokansa su ma duk ’yan tsintuwar ne, suka dubi wasu tumakai suna tafiya, ga ’ya’yansu, biye da su, sai wani a cikinsu ya ce: “Wayyo ni Allah! Yanzu fa gara dabbobin nan da mu saboda ko ba komai su sun san iyayensu, mu fa?! Wannan magana da ya yi duk sai ta motso musu bakin cikin da yake dankare a kirazansu, wasu daga cikinsu suka fashe da kuka, wasu kuma suka nutsa cikin kogon tunani, daga lokacin wani ya yi azamar zuwa hajji, ya yi ta kokari har Allah ya taimake shi, bukata daya ce jal ta sa shi zuwa hajji, ita ce yin addu’a ta musamman.

Bawan Allan nan tun da ya yi sallar azzahar da la’asar, a Arfa ya fara addu’a ba kakkautawa, yana cewa Ya ubangijina, ya mahallicina, ya masanin abin da yake boye, ya Ubangijin halitta, Ka san irin bakin ciki da damuwar da nake ciki, Ka san mawuyacin halin da wadannan la’anannu suka sa mu a ciki na bakin cikin duniya, ta hanyar aikata abin da ka haramta a littafinka mai tsarki wato ZINA daga nan sai ya fashe da kuka! Ya yi ta kuka kamar ransa ya fita… a biyo mu

01.24.10

ADDU’A TA GARI

Posted in Adduo'i at 9:01 pm by iyalina

Ya Allah Ka yafe mana,Kayi mana rangwami,Kaji tausayin mu, Ka karbi ibadunmu, Ka kuma saka mu a aljanna sannan kuma Ka tsaremu da wutar jahannama!!!

Daga Sa’adatu Mahdi

 

05.06.09

Allah yana son Masu kyautatawa

Posted in Nasiha da wa'azi at 12:42 pm by iyalina

“Ku kyautata Allah yana son Masu kyautatawa” (Bakara: 195)
¨ “Wanda ba ya girmama manyanmu,kuma ba ya tausayin kananamu ba
shi daga cikinmu” (Sahihul Jami’a)
¨ Annabi (SAW) ya ce: “Ku rika musayen kyuta (a junanku) sai soyayyar
(dake tsakaninku) ta karu.(Sahihul Al’adabul Mufrad)
¨ Annabi (SAW) yana ziyartar ‘ya’yansa a gidajen mazansu. Kai ma ka rika yin haka nan, sai ka dace da sunna, kuma soyayyar dake tsakaninku ta kara habaka.

05.05.09

SHAWARWARI!!!

Posted in Nasiha da wa'azi at 6:26 am by iyalina

Aljanna tana karkashin dugadugan mahaifa (mata) (Ahmad da Nasa’i)

 • Don isar da sakon nasiha, ga mijinki,ko mahaifinki rika ajiye masa KASET din da ya kunshi wannan sakon A CIKIN MOTA kusa da wurin sa kaset (ba tare da kin gaya masa ba)

• Annabi (SAW) yakan taya matansa aikin gida.

• Me kake so ka zama a nan gaba?

 • Kyautatawa danka yana karami,sai ya kyutata maka in ya girma

RIKA AIKAWA DA KAWAYENKI WADANNAN SAKWANNI TA WAYA !!!

Posted in Nasiha da wa'azi at 6:11 am by iyalina

Tsoron Allah shi ne tushen nasara a zamantakewar aure da tarbiyyah.
“Kar ku manta da mutuncin dake tsakaninku (Bakara:237 ) .
Namiji da bangaren HAGU na kwakwalwarsa yake tunani, mace kuma na DAMA. Ya za ki amfana da wanan bayanin a zamanki da mijinki?
Zama baiwar mijinki, sai ya zama bawanki
“Idan muslumi ya ciyar da iyalinsa don neman lada a wurin Allah, ta zama sadaka (Bukhari: 5351).
Gangancin yaro kuskure ne.
Wanda ya wahala yana yaro, in ya girma zai huta.

04.07.09

KARATUN JAMAI’A

Posted in Matasa at 12:34 pm by iyalina

       Jami’a tana daya daga cikin wurare da suke ba wa mutum ‘yanci, ma’ana ba mai takura masa, kuma ba a damu da abin da yake yi ba. Amma kuma idan aka duba jami’a wuri ne mai hadarin gaske in dai har mutum bai yi mata da gaske ba. Jami’a mahada ce ta mutune daban-daban, daga wurare daban-daban wadanda tarbiyyarsu da al’adunsu suka bambanta; saboda haka ya kamata dalibai musamman sababbi su lura da wadanda za su zauna tare a matsayin abokai, kawaye ko makamancin haka; don akwai mutane da za su batar da mutum in har bai yi a hankali ba, ko kuma shi bai yi kokarin jawo su zuwa hanya ta daidai ba; domin wasu manufarsu ta shiga jami’a ba wai samun ilimin da suka je nema ba ne, a’a, su dai kawai su sami yadda za su yi su lalata tarbiyyar ‘yan uwansu matasa ne. A yanzu da yawa daga cikin dalibai suna jami’a, amma ba su da wata manufa mai nagarta ta kasancewarsu a cikinta, da za ka tambayi wani dalibin ka ce me zai karanta a jami’a, sai ya ce: Ai komai aka ba shi karantawa zai yi. Abin tambaya a nan shi ne: Shin wai yin jami’ar ne ya zama dole, ko kuwa manufa ce babu! Ya kamata mutane su san cewa yin jami’a ba wai zama dole ya yi ba, sai dai don manufar samun ilimi mai nagarta domin taimakon addini da al’ummar musulmi, musamman saboda kalubalen dake fuskantar musulmi ta fuskoki daban-daban a cikin gida da waje. In aka duba bangaren mata misali, na ha]u da wasu sa’o’ina da ba su sami kyakkyawar shawara akan abin da ya kamata su karanta ba, a cikin ire-iren wadannan dalibai sai ka ga mace ta je ta dauki kamar Civil Engineering; (abin da ya kunshi koyar da yadda ake yin tituna, gadoji, dss). Ko kuma irin su Political Science da makamantansu, ni kuma ina ganin cewa gudunmawar da mace za ta bayar ta irin wad annan kwasa-kwasai ba su dace da dabi’ar ‘ya mace ba. A halin da muke ciki a yau, al’ummarmu tana bukatar mata wa]anda suka kware a fannonin aikin asibiti kamar likitanci, nurse da unguwarzoma da makamantansu; saboda haka ne ma nake da burin karanta aikin likita, kuma nake fatan Allah ya cika min burina, ya taimakamin akan samun nasarar shiga da kwarewa a wannan fannin.

FATIMA HUSAIN FALAKI

03.27.09

ALLAH YA GAFARTA WA WANCE !!!

Posted in Gidajen Manya at 8:24 pm by iyalina

Imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) bai yi auren fari ba sai da ya kai shekara arba’in; da ya tashi aure sai ya fara tantance gidan da ya kamata ya hada zuriya da su, sai aka ce masa akwai ‘yan mata biyu a gidan, daya kyakkyawa ce, dayar kuma idonta daya, sai ya ce wacce ta fi hankali? sai aka ce mai ido dayan, sai ya ce: ita za ku aura min. Zamansu ya yi dadi sosai. Bai yi wani auren ba sai da ta rasu.

 Yake cewa: Almarwazi daya daga cikin daliban imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) ya ce: wata rana imamu Ahmad ya ambaci iyalinsa bayan ta rasu sai ya ce: Allah ya gafarta wa wance, shekararmu ashirin tare amma ko sabani ba mu taba ba.

 

MAKKA BABBAN GARI HAR DA GONAR LANTARKI!!!

Posted in Almara at 8:10 pm by iyalina

In ji wani dan Fulani lokacin da yaje kasa mai tsarki domin yin aikin hajji bayan jirginsu ya sauka a filin jirgin sama na sarki AbdulAziz dake Jidda (kasancewar akwai fitulu da dama akan doron titin filin jirgin).

AN YI MUSU BUSHARA DA ALJANNA TUN SUNA DUNIYA !!!

Posted in Fagen Ilimi at 7:08 pm by iyalina

SUNAYEN SAHABBAI GOMA DA AMBATONSU YA ZO A HADISI GUDA AKA YI MUSU BUSHARA DA ALJANNA TUN SUNA DUNIYA:

1. Abubakar Assiddik ( Allah ya yarda da shi).

2. Umar Alfaruq (Allah ya yarda da shi).

3. Usman Ibn Affan (Allah ya yarda da shi).

4. Aliyu Ibn Abi Dalib (Allah ya yarda da shi).

5. Abu Ubaida Ibnul Aljarrah (Allah ya yarda da shi).

6. Abdul Rahman Ibnu Auf (Allah ya yarda da shi).

7. Azzubair Ibnul Awwam (Allah ya yarda da shi).

8. Dalhatu Ibnu Ubaidillah (Allah ya yarda da shi).

9. Sa’ad Ibnu Abi Wakkas (Allah ya yarda da shi).

10. Sa’id Ibnu Zaid (Allah ya yarda da shi).

 

03.26.09

MADUGUN MASU RAYUWA DON SU CI

Posted in Fagen Nishadi at 11:33 am by iyalina

Mutum mai hankali yana ci ne don ya rayu, amma bayin ciki irin su Ash’abu suna rayuwa ne don su ci! 

Ash’ab wani mutum ne da labarawa suke ba da misali da shi wurin kwalama da babakeri, da hadama da mutunta abinci sama da komai.

Daga cikin labarinsa:

¨ Wata rana budurwarsa ta tambaye shi ya ba ta kyautar zobe don ta rika tunawa da shi, sai ya hana ta, ya ce mata idan kina son tunawa da ni, ki rika tunowa kin tambaye ni zobe na hana ki!

¨ Ya taba yi wa wasu yara karya ya ce ana rabo a gidan wane, da ya ga suna ta tafiya can, sai ya ce a ransa kar fa a ce da gaske ne, sai ya ruga don ya riga su.

¨ Yana sahun sallah da wani shugaba, sai shugaban ya yi tusa daraaam sai shi kuma Ash’ab ya kama hanji ya fita kamar ya yi habo, da shugaban nan ya koma gida sai ya bi shi ya ce ba ni ladana, ya ce wane lada? Ya ce ladan tusar da ka yi; ko ka biya ni, ko in je gari in yayata in ce wannan tusar da ma kai ka yi ba ni ba!

Next page